Categories
Hausa Language Notes

Tsarin Rubutaccen Adabi

Rubutaccen adabi kamar yadda mukayi bayyani shi ne wanda ake kira da ‘Adabin zamani’ wannan shi ne adabin da masu ilimi suka rubuta a littafai don jama’a su karantasu kuma amfana.

Ilimin rubutu,  wato yin amfani da tsara wadansu alamomi a kan takarda ko wadansu abubuwa, kamar allo, ganye dutse  da makamantansu don sadar da wata magana ko sako, wacce dan Adam ya saba da  fadar ta da fatar baki, a kuma saurare shi da kunne, ya samu ne ga dan Adam lokaci mai tsawo, kuma dan Adam yana yin amfani da alamomin rubutu iri-iri a sassa daban-daban na duniya. Misali mutanen kasar China (sin) suna yin amfani da wadansu alamomi masu kama da zane, ko hoto don sadar da magana a rubuce tun shekara 3,500 da suka wuce. Su kuma Jafanawa mutanen kasar Japan, suna yin amfani da wata alama guda daya tak ta wakilci gabar kalma, wato ta yi aikin baki da wasali wajen rubutu magana tun kimanin shekaru 2,000 da suka wuce.

     Hausawa sun dauki irin tsarin alamomin da turawa da larabawa suke yin amfani da su. Wato alamomin nan na “abacada” suna rubutu maganarsu ta hausa da su. Watau hausawa, sun yi amfani da tsarin alamomin rubutu na Larabawa wajen maganganunsu, wannan irin tsari shi suke kira da “Rubutun Ajami”. Haka kuma, sun yi amfani da tsarin rubutun turawa na abacada, wajen rubuta maganarsu ta hausa, wannan shi suke kira da “Rubutun boko”.

Hanyoyin Nazarin Rubutaccen Adabi

 A wajen nazarin rubutaccen adabi, wato zube (labari) ko wasan kwaikayo, ko waka, ana yin la’akari da wadannan muhimman abubuwa:

  1. Zubi da tsari
  2. Jigo
  3. Bayyanin Jigo
  4. Warwarar Jigo
  5. Salon sarrafa Harshe

A wajen nazarin rubutaccen waka, tilas ne a kulla da wadannan abubuwa guda biyar a kan kowane bangaren rubutaccen adabi Ga misali:

  1. Zubi da tsari: Mai yin nazarin zai yi kokari ya fito da yadda marubucin wakar ya tsara ta, wato ya kula da yadda aka fara bude wakar, ko marubucin ya fara da addu’ar budewa, ko bai fara ita ba. Mafi yawan rubutattun wakokin  Hausa suna farawa ne da addu’ar budewa, inda ake neman taimako daga Allah ya dada ba da basira, da kuma yabon Annabi, kamar yadda malam sa’adu Zungur ya yi a farkon wakarsa ta Bidi’a inda ya ce:
  2.  “Ka daura niyya a kan waka kana addu’a

A’uzu Billah daga shaidan a kan bida’a.

2.Sannan kawo basmala bisa kan rikon sunna,

Ka biya da yin hamdala ita ce wajen jama’a

3.Dafa kawo salsala don kammala da’a

Ga wanda aikensa rahama ce wajen jama’a

4 Ka iyar da kalmar salatu zuwa ga Alaye,

  Da sallama ga sahabbai masu kyan dara’a

      Wannan ita ce ake cew addu’ar budewa. Sai kuma a kula da yadda marubucin ya rufe ita wakar, wato ko ya rufe ta da addu’a, ko kuma da bayyana sunansa a karshe.

(ii) Jigo: Jigo Dai shi ne manufar waka, watau  sakon da take dauke da shi a dunkule. A wajen nazarin waka, wajibi ne a gano jigon wakar a fito da shi a fili, a kuma fito da baiti ko a bayyana yadda mawakin ya gina jigon nasa a cikin baitocin wakar. Daga nan sai warwarar jigo, ana ne mai nazari zai yi kokari ya bayar da tasa fahimtar a kan jigon wakar, yana yin sharhi sosai tare da kowa misalai daga wakar. Idan an zo wajen nazarin waka za a ga misalai na yadda ake fito da jigo, da kuma warwarar jigo a nan gaba, cikin littafi na biyu.

  1. Salon sarrafa Harshe: A nan za a yi la’akari da yadda marubucin waka yayi amfani da harshe, ko yan da saukin fahimta ko ya yi wahala. Sannan kuma za a kara kula da yawan kalmomin aro na wasu harsuna kamar
  2.  

Larabcida turanci da marubucin ya yi amfani da su a cikin wakar. Da irin yadda ya nuna gwanintar harshe a cikin wakar ta wajen yin amfani da karin magana, da kirari. Sai kuma a lura da yadda marubucin yayi amfani da “lugogin Harshe” wato irin dabarun jawo hankali, kamar su:

  • Siffantawa
  • Kamantawa/Misaltawa/kwatantawa
  • Mutuntawa
  • Karagiya/Luguden kalmomi

Auna Fahimta

  1. Wajen rubutaccen adabi, bada muhimman  abubuwan da  ake la’akari da su?
  2. Yi bayani daya daga cikin su.

Tarihin rubutun hausa

          Kamar yadda ya gabata, an bayyana cewa rubutun hausa ya soma asalin ne ta hanyar amfani da alamomin rubutu na larabawa da na turawa. Yanzu sai mu dan leka mu ga dan takaitaccen tarihin wadannan  hanyoyin rubutu da hausawa suka  ara, suna rubuta hausa da su.

    Rubutun Ajami

Wannan ita ce hanyar rubutun da hausawa suka aro daga alamomin rubutu na larabawa, inda suke yin amfani da wadannan alamomi wajen rubuta maganganun hausa.

   Wannan hanyar rubutu ta samu ne a sakamakon zuwan addinin musulunci kasar hausa. Amma wani bayani ya nuna cewa tun kafin  Addinin musulinci ya shigo kasar hausa, an samu wadansu larabawa yan kasuwa da suka shigo kasar hausa do yin ciniki. Su wadannan larabawa yan kasuwa sun shigo kasar hausa don harkar kasuwanci, suka hadu da hausawa suna huldar ciniki, ta wannan hanya  ce, hausawa suka soma  koyon alamomin rubutun larabci, suna amfani da su wajen rubuta hausa.

  Rubutun Boko

Kamar Yadda addinin musulunci ya zama sanadiyar shigowar  rubutun larabci, Kuma rubutun larabci yayi sanadin samuwar rubutun ajami, haka shi ma rubutun boko ya shigo cikin makwabtan  hausawa na kudancin Najiriya ta fuskar addinin masihanci wato addinin Kirista. Harrufa na romawa Hausawa suka sake wa fasalin rubutu don su dace da ire-iren saututtukansu kamar dai yadda suka yi wa harrufan larabci.

Auna Fahimta

  1. Kafin zuwan ilmin boko ta wacce hanya ce hausawa ke rubutun adabinsu?
  2. Ta wani fuskar addini rubutun boko ta shigo?

Read our disclaimer.

AD: Take Free online baptism course: Preachi.com

Discover more from StopLearn

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading

Exit mobile version