Categories
Hausa Language Notes

Hanyoyin Kyautata Sana’o’ in dadai da na zamani

Kamar yadda zamani ke chanzawa ababe dayawa ke dauka salo ya kuma bi zamani. Hakannan ma ta harkar sana’a Misali:

  1. Sana’a Noma kamar yadda muka yi bayyani noma tsohuwar sana’a ce wanda kowa ya tashi ya sa me ta. Ka fin zamani ya chanza ababen da manomi yake amfani da shi ne Fartanya, lauje, margibi da ma hudan shanu. Amma kamar yadda zamani yake chanzawa ilimi kuma na karuwa. Wannan kuwa ya kawo sauki ga sana’ar noma ta wajen amfani da trakta wajen gwara filin noma banda wannan har ma shuki wani lokaci ba sai an yi amfani da fartanya ba akan amfani da mashuki da ake hada shi da tracta a turance ana kiran sa (planter machine). Chigaba da zamani ya kawo ya kyautatawa  sana’ar noma kwarai da gaskiye sabi da manomi guda yan kan noma abinci da ze ciyar da dubbin jama’a.

      Zamani kuma ya taimaka da kawo iri mai yi a cikin karamin lokaci misali idan iri na masara na da yakan dauki wata biyar ya nuna na zamani kuwa zai dauki lokaci kadan misali wata biyu da rabi zuwa wata uku.   

              Haka ma tawajen kiwo zamani ta sa an samo wa dabbobi abinci kala- kala wadda yake sa su girma da wuri kuma su haiyafa.  Bari mu dauki misali wajen kiwan kaji zamu ga cewa  ana kin-kisa kwai kaza da abida ake kira a turance (incubetor machine) wannan yakan kin-kisa kwai mai yawa a dan kankani lokaci. Abincin da ake basu kuwa na zamani ne ya kan sa su girma da wuri. Ta haka kasuwancin kaji yakan bunkasa sasai.

Sana’ar saka kuwa wata sana’a ce wadda mata suke yi sukan saka hula, rigan sanyi da dai sauran.  Ana anfani da kureshe wajan saka, yin saka sana’a ce wadda ke taiwaka wa mata. Zamani kuwa ta kyautata wa wannan sana’a ta wajen amfani da injin saka. Wannan yana taimaka ta wajen saka mai yawa a dan cikin lokaci.

 Attakaice ce dai zamani ya taimaka wajen bunkasa sana’o’ i da yawa.

Auna fahimta.

  Yi takaitaccen bayyani akan yadda zamani ta kyautawa sana.

Exit mobile version