Categories
Hausa Language Notes

Ire-iren Sana ‘o’ in Gargajiya

Sana‘o’ in hausa na gargajiya suna da yawa, baza a iya iyakance adadinsu ba. A nan ya kamata dalibai su tuna cewa anyi masu nazarin wadannan sana’o’ in gargajiya a littafi na biyu na jerin gwanon littatafan sabuwar Hanyar Nazarin Hausa don kananan makarantun Sakandare. Domin haka a wannan darasi za a yi bitar wadannan sana ‘o’i ne ga dalibai ta hanyar rarrabe musu su dalla-dalla don samun saukin ganewa.

   Idan aka dubi jimlar sana ‘o’ in gargajiya za a iya tantance su dangane da masu aiwatar da su, kamar sana ‘o’in da suka danganci maza da mata da wadanda suka yi tarayya da juna. Ga bayaninsu kamar  haka.

    Sana ‘o’ in Maza

Su ne wadanda yawanci maza ne suka fi yin su, ko da yake akan sami mata su yi su amma ba da yawa ba. Irin wadannan sana ‘o’ i sun hada da

  1. Farauta
  2. Gini
  3. Su(kamun kafi)
  4. Rini
  5. Sassaka
  6. Fatauci
  7. Tuki (mota /Jirgi)
  8. Noma
  9. Wanyanci
  10. Bokanci
  11. Dillanci

Sana ‘o’ i ne  wadanda ga al’ada mata ne suke aiwatar da su daga ciki akwai 

  1. Kitso
  2. Koda (casar hatsi /sussuka)
  3. Yin daddawa
  4. Kosai
  5. Suya cincin,  alkaki
  6. Suya gyda ko aya
  7. Dafa taliyar alkama
  8. Yin kuli-kuli
  9. Yin waina
  10. Saka

Sana ‘o’ in Tarayya

   Wannan nau’i kuma wasu sana ‘o’i ne wadanda aka yi tarraya  tsakanin maza da mata wajen aiwatarwa. Al’ada ta amince wa jinsin maza da mata su gudanar da su ba wata tsangwama ba. Kadan daga cikin wadannan sana ‘o’i su ne:

  1. Noma
  2. Kasuwanci
  3. Dillanci
  4. Ginin tukwane
  5. Maganin gargajiya
  6. Kiwo
  7. Waka
  8. Lambu

Auna fahimta.

  1. Menene Sana’a?
  2. Lissafa sana’ar mata uku
  3. Lissafa sana’ar maza hudu
  4. Lissafa sana’ar tarayya uku

Masu sana’a

r Gargajiya

A al’ada masu sana ‘o’ in gargajiya tamkar jini da tsoka ne tsakanin junansu, sukan hadu su taimaki junansu bisa hidimominsu na yau da gobe

 Mako na takwas: (week 8)

Batu (Topic) Bayanin wadansu Zababbun sana ‘o’ i


      1. NOMA

Menene Noma?

Noma na duke tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya tarar. Wannan shi ne kirarin sana’ar noma. Sana’ar noma ta bambanta da sauran sana ‘o’ in Hausawa. Bakamar  sauran sana’o’ in ba inda kusan kowace sana’a akwai mutanen da aka sani da ita, noma sana‘ar kowani mahaluki ce. Duk wanda aka ga yana sana’ar fawa ko sana’ar kira to lalle ya gada ne daga gidansu.  Amma noma sana’ar kowa ce a al’ummar hausawa. Da sarakai da malami da attajiri da talaka kowa ya gaji sana’ar noma.

    A takaice dai noma tsohuwar sana’a ce wadda kowa ya duniya ya tadda ta.

Ire- iren Noma

   Noma  ya kasu kashi biyu. Akwai dai noma da ake yi yanayin da damina ta sauka. Damina takan yi akalla wata biyar. Wannan lokaci ne ake yin aikin damina.

Wato a yi shuka ya nuna a girbe a kawo gida. Wannan shine kashi na farko na noma, wato noman damina. Kashi na biyu kuwa shine  irin noman da ake ci gaba da yi bayan daukewar ruwan sama a wurare masu dausayi da koramu. Irin wannan noma akan yi shi ta ban ruwa ne ga shukar. Wannan shi ake kira noman rani ko kuma moman rafi.

Kayan Noma Don ci

   Burin kowane manomi ne da akalla ya noma abincin da zai kai shi har karshen shekara bai je ma’auna ba. Gazawa ce ga magidanci ya yi noman da bai raba shi da awo ba.

     Manoma sukan noma kayan abinci  kamar su gero da dawa da wake  da masara da doya da rogo da dai sauransu. Bayan manomi ya ware wadataccen abinci don iyalansa wasu lokuta wasu manoma kan ware wanda za su sayar  a kasuwa.

Auna fahimta.

  1. Menene Noma?
  2. Noma iri nawa ka sani? Bayyanasu

Kayan Noma Don Sayarwa.

Haka nan bayan noma kayan abinci, manomi yakan noma kayan sayarwa kamar su gyada da auduga da ridi da dai sauransu. Kudin da ya samu daga kayan sayarwa da ya noma su ke taimaka  masa da sauran hidimominsa na shekara. Hidimomi na alheri da sauransu.

    Bayan wannan ma manomi yakan noma kayan rafi. Wadannan kuwa su ne kamar su tumatir da albasa da kubewa da tattasai da attarugu da yakuwa da dai sauransu. Irin wadannan kayan rafi ma akan yi amfani da wasu a gida ne, wasu kuwa a sayar a kasuwa. Sannan kuma akan yi hasafi da su ga sauran yan uwa da abokan arziki.

Kayakin Aikin Manoma 

    Kayan aikin manoma sun hada da sungumi da magirbi da fartanya ko hauya ko kalme da garma da lauje kai wani lokaci ma har da gatari.

 Wasu kayan aikin su ne manjagara ko mayayi. Akwai mandigiri ko kumbo don kaftu a fadama. Akwai magauji don yin kwarce. Akwai kuma ashasha wadda ake yin noma a tsaye da ita.
 

Auna Fahimta

  1. Lissafa kayan noma don sayar wa guda uku
  2. Rubuta kayan aikin manoma Guda uku(3)



2. Kiwo
Menene Kiwo?

Shi ma kamar sana’ar noma, kiwo na kowa ne. Wato ba a gadonsa. Kuma shi kiwo ba manya maza kadai aka san su da shi ba, har ma mata da yara suna sana’ar kiwo.

Akwai kiwon dabbobi kamar su awaki ko tumaki ko shanu ko raguna da dai sauransu.

Wasu sukan tanadi kiwon kaji ko agwagi ko kuma zabi.

Idan suka yi yawa akan tanadi mai aikin  kiwo musamman lokacin da damina ta fadi aka yi yawa aka yi shuka. Amma idan da rani ne kowa yakan sau awakinsa da tumakinsa domin babu tsoron za su shiga gonakin mutane su yi barna. Amma kaji da agwagi babu wani abin damuwa wajen kiwonsu, domin a nan gida ko kuwa sauran gidajen na unguwar suke kiwonsu ko ma a kwararo.

 Turkewa

Wannan hanya ce da mutum kan tsare dabba daya ko fiye tare da isasshen abinci don yayi musu kiwo na musamman ya sayar. Irin wannan turkewa takan kasance ko raguna ne ko kuma bunsura. Kodayake ba sai don sayarwa ba ma akan yurke irin wadannan  dabbobi domin wasu bukatu kamar na layya ko kuma suna. Amma idan shanu ne yawanci akan turke bajimi ne guda daya ko kuwa guda biyu. Idan su kai yadda ake so sai kwance a je a sayar da su da kudi masu dan kauri. Wasu kam sana’arsu ke nan ta turke shanu suna sayarwa. Wasu kuma sukan turke dawaki ne. Idan sun goya su sosai sai su sai da su ga mai so. Ta irin wannan hanya ce ake kiwata dawakin sukuwa domin masu shawara irinsu. Sannan saraki ma sukan sayi goyayyun dawaki don amfani da su.

   Sauran makiwata irin na sauran dabbobi da tsuntsaye ma sukan yi hakan don biyan bukatunsu na kudi idan wata bukata ta taso musu. Idan irin wannan hali na bukatar kudi ya zo sukan kama daya ko biyu gwargwadon bukatar tasu domin su sai dasu  su sami kudin biyan bukatu.

  Duk da haka ba a mantawa da masu kiwo na nishadi. Wato irin kiwon nan na kyanwoyi ko beran masar kai har ma da doki. Akan kiwata zomaye ko tsuntsaye kamar aku da dai sauransu.

    Auna Fahimta

  1. Menene Kiwo?
  2. Bada misallan dabbobin da ake kiwo guda hudu(4)

3. Kasuwanci

Menene Kasuwanci?

A saya a sayar shine kasuwanci. Wato a nan mutum ya fitar da kudinsa ya sayi kadara, sanan wani lokaci ya fitar da wannan kadarar ya sayar shi ne kasuwanci. Mai irin wannan harka shi ne ake dan kasuwa idan mace ce kuwa akan kira yar kasuwa.

  Kasuwanci ba ya yuwuwa sai da jari. Jari shi ne ake amfani da shi don sayen kadarar da za a sayar. Dan kasuwa dole ya rike jari domin ya rika jujjuya shi. Wato yakan yi amfani da jarin domin sarin kayan sayarwa Sannan idan ya sayar da kayan  ya yi  amfani da jarin domin sarin kayan sayarwa. Sannan idan ya sayar da su,sai ya kidaya ya gairin ribar da ya samu. Yakan gane haka bayan ya sayar da kayan, ya kidaya kudaya kudinsa, ya ware uwar kudin ya kuma ga irin abin da ya hau. Idan wani abu ya hau yakan ce an sami amfani idan kuwa uwar kudin ba ta fito ba sai ya ce, ya fadi. Saboda haka nasarar kasuwanci ita ce a ci riba. Amma idan wani dan kasuwa ya dinga faduwa a harkar saye da sayarwarsa jarinsa kullum raguwa yake har ma ya kai ga halin jarin ya bata, irin  wannan hali akan ce mutum ya karye. Wato ba shi da sauran jari a hannunsa.

  Dan kasuwa yakan ba da lamuni ga abokan ciniki. Haka tana faruwa ne idan ya kai kayansu wurin sayarwa kuma su masu sara su sayar ba su da wani kudi a hannunsu da za subiya nan take, sai ya lamunce musu sai su ma sun sayar sannan su kai masa nasa kudin. Wani lokaci kuma dan kasuwa yakan bada wasu kayayyaki kamar kayan haja ya lamunci abokan cinikinsa sai an fara hada-hadar kaka sannan ya zo ya karbi biyan bashinsa. Wannan hayar ma wani lokaci wasu yan kasuwar takan zame masu sanadiyar karyewa. Wani cinikin kuwa juye ban kwaryata ake yi. Hakan takan faru ne idan akwai matsnancin dukatar wannan kayan sayarwa. Wato a nan ciniki kan zama kudi hannu ne.

  Ciniki yakan dauru tun daga tayi ana albarka kara dai, a’a sai ka sallama.

Akan ce to la’ada ciki ko kuwa la’ada waje? Idan la’ada ciki ne to mai sayarwa shi ke biyan la’adar idan kuwa la’ada waje ne to mai saya shi ne zai bada la’adar.

    4. Dillanci

Menene Dillanci?

 Dillanci sana’a ce ta karbar kayan mutum a sayar masa sa’annan shi kuma mai kayan ya biya mai sayarwar ladan dawainiyar da ya yi.

 Yadda Ake Dillanci

  Idan Bahaushe yana da abin da zai sayar to yakan wakilta wani mutum da yake kwararre ne ta fuskar ciniki irin wadannan kayan. Dalili kuwa wannan mutum da ake kira dillali shi ya san halin kasuwar wannan kayan. Don haka sai ya karbi kayan da ga hannun mai sayarwa ya shiga cikin gari zuwa wuraren da ya san za a bukaci wannan kaya ya kai sayar. Yawanci idan tayin ya yi wa mai kayan dadi yakan ce a karbo awalaja. Idan ko bai yi ba sai ya ce albarka. Shi mai sayen da ma yakan fara ciniki da cewa nawa aka taya? Idan an fada masa sai ya nemi ragi ko kuwa ma ya dan kara. Wani lokaci idan ya tsaya yana shawarwari sai dillalin ya ka da baki ya ce, a taya kwabo ma shi alabarka ce tasa kawai. To da zarar an sallamar da kayan akan ce la’ada ciki ko waje, sa’annan a samu a daidaita.

     Su wa ke yin Dillanci?

   Banamiji kadai ke sana’ar dillanci ba, Mata ma na yi. Irinsu ake kira dillaliya. Wannan kuwa yawanci kayan mata ta fi karba don sayarwa. Kuma tana bi ne gida-gida tana nuna kayan dillancinta.

    Yawancin kayan dillali tufafi ne irin na maza. Dillaliya kuwa takan dau tufafi na mata. Haka kuma takan karbi kayan adon hannu ko na wuya ko na kunne ta kai talla. Takan ma dau kwanuka ko tasoshi da sauran kayan adon daki ta rika sayarwa. Shi ma dillali namiji yakan sayar da irin wadannan kaya na mata.

    A halin yanzu dillanci bai tsaya kan irin wadannan  kaya da aka ambata ba Dillalai sukan yi dillanci abubuwa kamar su rediyo, da agoago da gidaje kai har ma da motoci da dai sauransu.

   Muhimmancin Dillalai

  Babban muhimmancin dillalai shi ne sasantawa tsakanin mai abin sayarwa da kuma mai sayensa. Kuma ko da rigima ta tashi tsakanin mai saye da mai sayarwa, shi ne babban mai sheda.

Auna Fahimta:

  1. Menene Dillanci

Menene muhimmancin dillanci

Click here to ask a question and get an answer published in the forum. Read our disclaimer.

Get paid for every topic you create in: Shoutam.com Forum!MAKE-MONEY