Categories
Exam Lessons Hausa Language

Ma’anar sana’a

Sana’a hanya ce ta amfani da hikima a sarrafa albarku da ni’imomin da dan Adam ya mallaka don bukatun yau da kullum. Don haka ke nan ana’a wata abu ce wadda mutum ya jibinci yi da nufin samun abin masarufi don gudanar da harkokin rayuwa. Sana’a abu ce wadda ta danganci tono albarkatun kasa da sarrafa hanyoyin kimiyya da fasaha da ni’imomin da suke tattare da dan adam da sha’anin kasuwanci na saye da sayarwa da ciniki da sauransu. Sana’o’ in su ne mafi girma matsayi da hausawa suke amfani da su don yin dogaro da kai, su samar da abubuwan da suke bukata. Ta hanyar abin da bahaushe ya samu daga sana’arsa ne yake musanyawa ya mallaki abubuwan da ba zai iya samarwa kansa ba.

  Mako  na shidda  (Week 6)

Batu (Topic)Muhimmancin Sana’a

 1. Biyan bukata
 2. Dogaro da kai
 3. Kare mutunci
 4. Samun abun masarufi
 5. Hana zaman banza
 6. Samar da aiki
 7. Koyar da sana’a
 8. Habaka tattalin arziki
 9. Kyautata hulda da juna
 10. Rufe asiri
 11. Ya sa zumunci tsakanin mai saya da mai sayarwa
 12. Kwautata wa al’uma
 13. Kasuwaci yakan sa gari ya girma(misali kano da birnin iko)
 14. Yakan sa chunaya tskanin kasa da kasa Misali Nijeria da China
 15. Samun ci gaba.

Auna Fahimta

1.Menene Sana’a

2. Lissafa muhimmancin sana’a guda biyar(5)

  Aikin karshen mako

Karanta wannan takaiccen labarin sai ka amsa tambayoyin da ya biyo baya.

Muhimmancin sana’a ga ‘yan uwa mata

Daga Maimuna Yusuf Ali, No 1, Lemu rd, Tudun wada Zariya

Idan aka ce sana’a akwai sana’o’i, iri daban-daban. Mu dauki misali kamar sakar riga ta hannu na ‘fins’ ko kuma na kwarashe. In har uwargida za ta cire kunya ko in ce kyuya ta rinka yin saka, to labudda za ta samu ci gaba domin na yi na ga nasara, don ba zan manta da yadda na fara saka ba.

Don akwai wani lokaci da wata matsala ta dame ni, sai wata ‘yar uwa, kuma aminiyata ta ga halin da nake ciki, sai tana ganin mafita kawai tunda na iya saka me zai hana in rinka yi? Sai ni kuma na ce mata “Amina,” don sunanta kenan, “ba ni da inda zan rinka sayarwa.” Sai ta ce “Maimuna in dai matsalarki na gurin sayarwa ne, to ki rinka yi, in Allah ya yarda ni zan rinka dauka in kai miki makarantarmu,” don lokacin tana karatu ne, kuma tana karantarwa. Sai na ce to, don muna tafe ne a kan hanyar zuwa gidan Jagoranmu Malam Ibrahim Zakzaky.

Da na dawo gida sai na ce gaskiya maganar Amina ita ce gaskiya, kuma ga shi ba ni da kudi. Sai ta ga kwana biyu ban yi ba, sai muka kara haduwa, sai ta ce “Maimuna ya maganar saka?” Sai na ce mata gaskiya ba ni da kudi ne. Ta ce kamar nawa zai yi miki? Sai na ce ni ko nawa na samu. Sai ta ba ni har Naira dari uku. Da su na fara yin saka. Da ikon Allah ma ba ta fara dauka ba, sai mutane suka ga yadda sakar take, sai mutane suka rinka siya. Kowa ina yi musu suna saye. Da haka Allah (swt) ya rufa mani asiri ta hanyar saka lokacin da na nemi rufin asirinsa.

Sai dai kuma yanzun ba na yi kamar yadda nake yi da, saboda matsalar yara, amma ga wanda ya ga yana da lokaci, in har ‘yar uwa na son yin sana’ar ta koyi saka ko da ko huluna take yi, in ba ta iya yin saiti duka ba, da dan wannan sai ka ga ‘yar uwa na dogoro da kanta don samun ci gaba.

Abin nufi ina fata ‘yan uwa mata za su dauki wannan shawara don su amfana da ita kamar yadda na amfana da ita. To ina ganin ya kamata in sa aya sai mun sake saduwa. Don in Allah ya yarda zan ci gaba da ba ku shawara kan abin da zai taimake mu a rayuwarmu baki daya. Kuma ina mai rokon Allah ya yi mana jagoran kan abin da ya fi zama mafi alheri ga mu baki daya.

Tambayoyi

1.Wa ya rubuta wannan labari?

2. Ba muhimmancin sana’a guda(1)

3. Wace sana’a ce Maimuna ta soma a cikin wannan labari?

4. Wani matsala ta somu kafin ta soma sana’ar?