Categories
Exam Lessons Hausa Language

Ma’anar rubutaccen adabi

Ma’anar rubutaccen adabi shine adabin zamani. Ana kiran wannan adabi ‘Rubutaccen adabi’ saboda da can can, tun asali, a rubuce ake tsara shi. Kuma ana kiransa ‘Adabin zamani’ Saboda bai dade sosai da shigowa ba kamar adabin gargajiya. Rubutaccen adabi ko adabin zamani ya samu ne bayan da hausawa suka iya rubutu da karatu. Hausawa kuwa, ga alama ba su iya karatu da rubutu ba sai bayan da musulinci ya shigo kasar hausa da kuma bayan turawa suka zo.

     Musulinci ya shigo kasar hausa ta hannun larabawa da mutanen melle. Shi ko musulinci yana amfani da harshen larabci. Don haka da musulinci ya shigo kasar hausa, sai hausawa suka koyi rubutu da karatu irin na larabci. A hankali a hankali kuma suka kirkiro rubutun hausa da harufan larabci. Ana kiran irin wannan rubutu da sunan “Rubutun Ajami”  Da rubutu ajami ne hausawa suka fara rubuta wakokin  addinin musulinci da hausa.

   Daga baya turawa suka shigo kasar hausa suka kafa mulkin mallaka. Su ma da suka zo sun taimaka wa hausawa wajen kirkiro rubutun boko. Shi kuma rubutun boko yana amfani da haruffan turawa. Da aka sami rubutun boko kuma sai aka shiga rubuce-rubucen littattaffan labarai, littattaffan koyon karatun boko, da wasan kwaikwayo, da sauransu.

3.  Mako na uku (week 3)

Batu (Topic)  Rukunonin rubutaccen adabi

Rubutaccen adabi ya rabu zuwa gida uku, kamar haka :-

  • Rubutun wakoki

Wadannan su ne wakokin da aka rubuta da ajami. Wadannan wakoki da aka rubuta da boko, wadanda bayan addini, suna kuma magana a kan harkokin duniya.

  b) Rubutun Zube

   Wannan shi ne rubutu wanda aka yi shi ba cikin tsarin  waka ba, misali kagaggun larabai wadanda ake karantawa don nishadi da kuma koyon zaman duniya da wasa kwakwalwa. Su wadannan labarai yawancisu littattafai ne wadanda ana fara yin su ne bayan da turawa suka kafa mulkin mallaka kuma hausawa sun iya karatu da rubutun boko.

c) Wasan Kwaikwayo

Wadannan wasanni ne da ake shiryawa a rubuce. Akwai kuma wasan kwaikwyon da ake shiryawa a rubuce don rediyo, akwai na talebijin , akwai kuma wanda ake yi a dandamali don yan kallo su gani.

 Rabe-raben Rubutaccen Adabi

Kowane  dan adam da irin baiwar da allah ya yi masa a kan kusan kowace harka ta rayuwa. A fannin adabi haka abin yake, cewa wadansu Allah ya yi masu baiwar nuna fasaharsu ga al’umma a wannan bangare ta hanyar rubutu. Ta rubutun ma akwai inda kowanne yake irin ta sa baiwar. Dangane da wannan akwai kashi uku na nau ‘o’ in rubutaccen adabi.

  Na farko dai akwai wadanda su ke da baiwar iya shirya labari, Wato ta irin  wadannan  labarai suke nuna fasaharsu ta ba da nishadi da kumma hannunka mai sanda ga al’umma. Irin wannan nau’i na rubutaccen adabi ake yi wa lakabi da zube. Don haka Zube bangare ne na rubutaccen adabi.

   Na biyu kuwa shi ne irin wadannan da ke da baiwar iya waka. Kamar zube waka ma ta hanyarta akan sami nishadi da kuma hannuka mai sanda. Ita ma dai wani bangare ne na rubutaccen adabi.

  Na uku kuwa shi ne Karaminsu a duniyar Hausawa, wato rubutaccen wasan kwaikwayo. Wajen bambance shi da irin wasan kwaikwayo na asali na hausawa, sai aka yi masa lakabi da wasan kwaikwayon zamani. Don haka wasan kwaikwayo na zamani ma bangare ne na rubutaccen adabi a al’ummar hausawa

  Amfanin Rubutaccen Adabi

  Adabi a rubuce ko kuma azanci a rike da kowanne ciki akan sami nishadi ta karanta shi ko kuwa sauransu. Saboda haka nishadi na daga cikin irin amfanin da ake samu daga rubutaccen adabi. Bayan nishadi kuwa wani babban amfanin adabi shi ne isar da wani sako na musamman. Irin wannan sako kuwa daga tunanin mawallafin wannan adabin ne yake.

  Wani babban amfanin rubutaccen adabi kuwa shi ne adana shi adabin. Wato a nan,  ba kamar azancin da ke ka ba, muddin dai abu a rubuce  yake, to ba za a sami ragi da kari ba. Yadda aka rubuta shi, komai dadewar zamani idan ak dauko shi, za a tarar cewa yadda aka ajiye shi haka za a same shi wato ba dadi ba ragi.

Auna fahimta:

  1. Menene rubutaccen adabi?
  2. Lissafa rukunonnin adabi guda uku (3)